Duk wanda ya saurari firar da gidan radiyo Arewa (Arewa Radio) yayi ranar Asabar da safe da shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Babangida Little yayi, zai fahimta cewa Little bai fahimci shugabanci ba.
Nayi wannan harsashene saboda yadda naji Babangida Little yake magana a firar kamar da kudinsa na aljihunsa yake gudanar da kungiyar Kano Pillar din bba kudin gwamnai ba, domin naji shugaban yana magana da buga kirji a firar kamar wani soja ba dan siyasa ba.
Yakamata Babangida Little ya sani cewa dan siyasa nema da jawo jamaa yake ba tarwatsa su ba. Nunawa ba wanda ya iya babban kuskurene wanda yana tare da dana sani.
A firar naji Babangida Little na nuna cewa a wajensa yan kwamitin gudanarwar da aka nada su tare ba dole bane su san komai da zaayi a kungiyar. Wannan babban kuskure ne domin gwamnati ta nada sune suyi aiki tare.
Idan da gwamnati so take Little yayi aiki shi kadai ba da yan kwamitin gudanarwa ba, da baza tayi tunanin nada masa yan kwamiti ba.
Waccan kuskurenne da ya kaishi daukar mai horarda da yan wasa Abdu Maikaba shi kadai ba tare da sahalewar sauran yan kwamitin gudanarwarba kungiyar ba yakai kungiyar Kano Pillars halin da ta sami kanta yanzu.
Kuma shine a cewarsa ya sashi bawa Maikaba wuka da nama wajen daukar yan wasa da kuma kudin da zaa biya yan wasan da shi kansa Maikaba ba tare dda sahalewar kwamitin gudanarwarba.
Shugaban ya fada kai tsaye shi kadai ya kawo Maikaba ba tantancewa da sahalewar yan kwamitin da gwamnati ta nadasu tare. Wannan laifine wanda yakamata gwamnati ta bincika.
A firar tasa Little ya kuma tabbatar da cewa haka kuma zaici gaba da tsarin shugabancinsa bazai tuntubi kowa ba sai dai kawai ya sheda musu abinda yayi. Wanda wani babban kuskurenne zai sake tafkawa.
Da kuma yake magana akan kungiyar magoya baya, Little bai nuna girmamawa garesu ba duk yasan cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da Pillars ke samu.
Bugu da kari yawansu da kudinsu sukeyi kuma suke kashewa don cigaban kungiyar da kuma samun nasararta.
Nunawa magoya baya dan yatsa da Little yayi shima babban kuskurene domin zai iya sama masa rashin nasara a shugabancinsa nan gaba.
Haka kuma, idan da tun da farko Little ya kafa kananan kwamitoci (Sub-committes) kamarsu Technical, da saurarsu a tsakanin yan kwamitin gudanarwar tasa da wasu kwararrun mutanen gari da Kano Pillars bata sami irin wannan matsalarba.
Domin sai yan kwamitin sun gana da kuma tantance kowa zaa kawo kafin ya fara aiki ko kuma ya zama dan wasa a kungiyar. Wannan zaisa a sami gagrimar nasara domin masu hikima sunce, mai shawara aikinsa baya baci.
A kashe, ina ganin idan har Babangida Little bai canja tsarinsa na daukar shi kadai ya iya ba, to lalle yanzu ya fara samun matsala wanda kuma ba dole guguwar ta rinka masa dadi ba.
Allah yasa gwamnati tayi nazari ta nada masa kwararrun mutane wadanda zasuyi aiki tare kuma su sami dimbin nasara, to amma san iyawa da son kai yasa yana ta zizzille musu, to ya sani fa, irin wannan san iyawarne yake kai fara ko tururruwa bakin kadangare.