Yan mintuna da bada labarin cewa dan wasan gaba na Kano Pillars Yusuf Abdullahi Tsamage ya kusa samun nasarar shiga kungiyar wasa a kasar Poland, rahotanni na cewa a yanzu haka Yusuf Tsamage ya dawo gida Nigeria.
A wata hira da Sharif Zaharaddeen Kofar Nasarawa, babban jami’in watsa labarai na kungiyar Kano Pillars ta wayar tangaraho ya bayyana cewa dan wasa Tsamage ya dawo gida Nigeria shekaran jiya.
Kofar Nasarawa ya kuma tabbatarwa wannan kafa cewa isowarsa gida keda wuya dan wasan ya zarce Abuja saboda gayyatarsa da mai horar da yan wasa na Flying Eagles, Ladan Bosso yayi.
“Ina tabbatar maka cewa Tsamage ya dawo kasa Nigeria kuma a haliin yanzu yana Abuja wajen sansanin horar da yan wasan kungiyar Flying Eagles” cewar Kofar Nasarawa.
Sharif Zaharaddeen Kofar Nasarawa ya kuma shedawa wannan kafa cewa ko jiya Tsamage ne yayi na farko a gasar gudu da akayi tsakanin yan wasan Flying Eagles din.
A cigaba da bibiyarmu don samun labaran wasanni