Tun lokacin da al’amuran kungiyar Kano Pillars suka shiga wani hali marasa kyau da dadin ji saboda rashin nasarar da kungiyar keyi a gasar pirimiya ta kasa watau NPFL, wasu da dama nata kiraye-kirayin rushe hukumar gudanarwar kungiyar.
Wasu na ganin cewa tunda shugabannin Kano Pillars sun kasa dauka da sauke nauyin da gwamnati ta dora musu, yakamata gwamnati ta rushesu da kuma sauyasu da wasu.
Wani rahoto ya nuna cewa tun fara jin irin wadanan kiraye-kiraye ne mutane dabam-dabam masu son mukamin shugabancin kungiyar ke ta tururruwar da dafdala wasu a offishi wasu kuma a gidan kwamishinan matasa da wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso don samun amincewarsa na zama daya daga cikin shugabannin kungiyar.
Wasu kuma wadanda basu da dama ko fada a wajen kwamishina Kwankwaso rahotanni ya nuna cewa suna bin jigajigai da manyan jami’en gwamnati dana jamiyyar NNPP don samun zama daya daga cikin yan kwamitin gudanarwar kungiyar ta Kano Pillars.
Wasu ma a cewar wata kafar, dunguma zuwa ofishin mataimakin gwamna, kwamraid Aminu Abdussalamu Gwarzo sukayi don sashi ya saka baki wajen tabbatar da samun mukaman kungiyar Kano Pillars din.
Rahoto ya kuka nuna cewa cikin masuyin zarya zuwa ofishin kwamishina Kwankwaso kullun-kullun don neman shugabancin Kano Pillars din, akwai daya daga cikin tsofaffin shugabannin kungiyar.
Haka kuma rahotanni sun nuna akwai kuma wasu daga cikin tsofaffin yan kwamitin gudanarwar kungiyar na baya wadanda suke ta shishshigewa kwamishina don samun matsayi a kungiyar Kano Pillars din.
Wani rahoton kuma ya bayyana cewa hatta wasu daga cikin yan kwamitin gudanarwar kungiyar masu ci yanzu na daga cikin masu nema idan an rushesu, to a basu dama domin suna ganin suna da yadda za suyi tagomashin kungiyar ya dawo.
Amma saidai a lokacin da wasu mutanen ke ganin cewa canjin shugabancin kungiyarne kawai mafita, mu aganinmu canjin ba shi bane a’ala domin a baya da aka sami kai cikin irin wannan yanayin, anyi canjin amma baiyi wani tasiri ba.
Nan baya kadan irin wannan ibtala’in ya taba fadawa kungiyar wanda yasa gwamnatin baya rushe hukumar gudanarwar kungiyarkarkashin shugabancin Jibrin Jambul da kuma bawa tsohon shugaban hukumar wasanni ta Kano, Alhaji Ibrahim Galadima ragamar gudanar da kungiyar wanda babu abinda ya sauya.
A karshe ma dai sai da kungiyar ta fado matsayi na kasa na NNL kafin sabuwar gwamnati ta shigo kuma aka samu kungiyar ta komo matsayinta na yanzu.
A ganinmu kamata yayi gwamnati ta fara kafa kwamiti na masana don bin ciko dalilai da abubuwan dake damun kungiyar sannan abi abubuwan da suka zayyana daya bayan daya don mayarda kungiyar tsayawa da kafafunta.
A kullum muna fada cewa idan anaso kungiyar Kano Pillar tayi abinda akeso to sai an mata abinda yakamata.
Abu na farko da zaayi shine ayi ko a tafiyar ko gudanar da ita yadda ake gudanar da sauran kungiyoyi kwallon kafa a sauran jahohi ko kuma kasashe na fadin duniya.
Irin yadda gwamnati ke bawa kungiyar Kano Pillars kudi don gudanar da harkokin kungiyar gutsi-gutsi ko guntu-guntu ba daidai bane kuma ba tsari a ciki.
Yin hakan na hana shugabannin kungiyar samun nutsuwa da hangen nesa da kuma shiri da wuri don gudanar da ayyukan kungiyar.
Akoda yaushe muna bada shawarar duba kasafin kudin kungiyar na shekara da kuma amincewa da shi, wanda daga nan sai a sakar musu kudi gwargwadon iko don su cigaba da gudanar da harkokinsu ba tare da zuwa wajen gwamnati sati-sati ba don karbar kudin tafiya ko kuma shirin wasan gida ba.
Ina tabbatar muku cewa babu wata kungiyar da ake gudanar da ita yadda ake gudanar da Kano Pillars a fadin kasarnan baki daya. Wannan shine abu na farkpo da gwamnati zata gyara idan anaso aga kokarin kungiyar nan gaba.
Ko zuwa wasan da kungiyar da tayi na baya-bayannan zuwau garin Aba, wasansu da Enyinba baa sallamesu sun tafi da wuri ba duk da nisan garin domin sai ranar Jumaa suka tafi wasan da za suyi ranar Lahadi. Ta yaya akeso aga da kyau da irin wannan tsarin?
Kaucewa irin wannan lamari da yanayi ne kadai zai ceci kungiyar Kano Pillars ba wai canje-canjen shugabannin kungiyar ba.
Domin bincike ya nuna cewa yawancin masu so da neman mukamin shugabancin kungiyar ba wani abu na musamman garesu ga kungiyarba sai dai son abin duniya da tarin son zuciyarsu kawai.
Kamar yadda na zayyana a cikin wannan rubutun, kamata yayi gwamnati ta fara neman shawarar masana don sanin yadda zaa fidda kungiyar daga cikin wannan mummunan hali da ta shiga ba canjin shugabanciba.
Allah yabamu saa, amen.
