Tun bayan samun labarin rashin nasarar dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars mai suna Yusuf Abdullahi Tsamage yayi a kasar Noway don cigaba da wasan kwallon kafa wanda yasa dan wasan sake nausawa wata kasar mai suna Poland, rahotanni na tabbatarwa wannan kafa cewa Tsamage ya kusan dacewa.
Wata majiya ta bayyanawa wannan kafa ta www.sportseye.ng cewa tsallakawar Yusuf Tsamage kasar Poland ke da wuya tauraruwarsa ta haska inda kungiyoyi kusan uku zuwa hudu suka gaiyaceshi izuwa wasan gwaji don duba yiyuwar daukarsa a kungiyoyinsu.
Duk da bamu sami cikakkun sunayen kungiyoyinba, majiyar ta nuna cewa kungiyoyin duk sun nuna gamsuwa da hazaka da kaifin basirar dan wasan kuma a shirye suke da su daidaita da wakilin dan wasa Tsamage don daukarsa daya daga cikinsu.
Duk kokarin samun dan wasa Tsamage ko wakilinsa do tabbatar da wannan muhimmin labari yaci tura domin kasa samun wata kafa ko wayar tarho da zamu same daya daga cikinsu.
Amma a cigaba da saurarenmu don tabbatar da gaskiya ko akasain wannan labarin.