Akalla kungiyoyin kwallon kafa fiye da hamsinne daga fadin yakin kananan hukumomi 44 na jihar Kano ne zasu shiga wasan gasar taya gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara daya akan gadon mulkin jihar Kano.
Da yake magana akan gasar wadda ake ganin baa tabayin irinta a jihar kano ba saboda yadda aka shiryata, wanda ya shirya gasar wanda kuma shahararren dan jaridane kuma daya daga cikin hadiman gwamna Abba Kabir Yusuf ne, mai kuma mikamin (SR Special Duties) na gwamnan Kano, Malam Muhammadu Wasilu Kawo ya bayyanawa wannan kafar cewa mukaddashiyar shugaban gidan talabijin ta ARTV, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ce ta dauki nauyin gasar.
Gasar wadda akesa ran farawa a farkon wanna watan, zaayi kwana talatin ana fafatawa tsakanin kungiyoyin da sukayi rijistar shiga gasar na fadin yankin jihar Kano.
Wasilu Kawo ya kuma bayyana harabar gidan Talabijin na Abubakar Rimi dake Hotoro ne a inda zaa rinka gudanar da wasan.
Shugaban gudanar da gasar ya kuma bayyana cewa kimanin Naira miliyan biyu zaa kashe wajen gudanar da wasan mai tarin tarihi da nishadantarwa.
“Kananan hukumomin Kumbotsu da ta Gwale ne zasu buga wasan farko na gasar,” cewar Muhammad Wasilu Kawo.