Yanzu-yanzun nan shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya ayyana dakatar da mai horar da yan wasan kungiyar Abdu Maikaba.
Wata majiya ta bayyana dakatarwar da kuma kafa wani kwamiti wanda zai bincikeshi a inda idan aka sameshi da laifi to zaa ladafttar dashi.
Duk da yake baa fadi dalilin dakatarwar da akayi masa ba, amma ana zargin maganganu da Abdu Maikaba ya furta a lokacin wani taro da kungiyar magoya bayan Kano Pillars sukayi a cibiyar yan jaridu ta jiha ne ya jawo dakatarwar.
A jira kadan..