Duk da naji labarin cewa shugaban hukumar gudanarwar Kano Pillars, Alhaji Babangida Little na tsame kansa daga laifin tunduma kungiyar Kano Pillars cikin rudanida rashin tabbas saboda aiwatar da tsarin yan wasan gida kawai, ni har yau ina kan bakana cewa su biyunnan sune da laifi.

Kowa yasan yadda da farko shugaba little ya daura yaki ko kuma ya ja layi da yan majalisar gudanarwar kungiyar da gwamnati ta nadasu tare, a inda shugaban ya tayin harkokinsa tare da jami’in da Hukumar Wasanni ta jiha watau Sports Commission ta nada ba wanda gwamnati da kanta ta nada ba.

Kowa kuma yasan yadda shugaba Little ya dauke offishin kungiyar Kano Pillars ya maida offishin Hukumar wassanni ta jiha inda yata harkokinsa shi kadai ba tare da sauran yan kwamitin da gwamnati ta nada masa ba.

A wannan lokacinne fa Little ya nada Abdu Maikaba da kuma kaddamar dashi ga al’ummar jihar Kano a offifishin mataimakin gwamnan jihar Kano.

Tunda ya gabatar da Maikaba, Little bai kafa kwamittin Technical bawa kwamitin dama da fawa don suyi aiki tare da  Maikaba ba.

Mun sani bar wa Maikaba wuka da nama da shugaba Little yayi wajen kawo yan wasa ya jefa kungiyar Kano Pillars cikin yanayi maras kyau. Saboda kowa yasan son zuciyar mu yan Nijeriya idan muka sami dama.

Rashin kafa babban Technical kwamiti mai kunshe da gogaggun mutane masu kima da sani da kuma ilmin abin yasa Maikaba yin yadda yakeso.

Hakan kuma kowa yasan kuskurene a wannan kasar kabaiwa mai horar da yan wasa irin waccen damar domin son zuciyarsa zaiyi. Da tunda fari da shugaba Little yayi abinda yakamata, da  baazo wannan bigiren ba.

Saboda haka ni haryau inanan akan bakana da Little da Maikaba sune suka tsunduma Kano Pillars cikin wannan hali da kungiyar ta sami kanta a ciki. Sai dai a iya gyarawa nan gaba.

Shawarata nan gaba shine, a jihar Kano munada mutane gogaggu, masu girma da masu mutunci kum masana harkokin kwallon kafa wadanda nasan mai horarda yan wasa bazai iya bude musu ido da juya su ba.

Irin wadannan mutanen yakamata a zakulo a nadasu a Technical kwamiti don su rinka duba yaran da zaa dauka da kuma yan wasan da mai horarwa zai rinka sawaa a wasanni.

Amma ku menene raayinku…

By Sani Yusif

I was at the production unit of the Triumph Publishing Company, Kano but my keen interest in sports journalism made me to be sports writer and maintained a sports column called (Sports Eye) after my mentor Sani Muhammad Zaria transferred his service to New Nigeria newspapers in Kaduna. And when the government closed the Triumph in 2012, I was transfered to lectured DTP in the Department of Printing Technology of Kano State Polytechnic. And now that I retired, i used to visit the institution weekends for part-time lecturing.