An nada Farfesa Musa Garba Yakasai wanda ake kira Farfesa AA a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na hukumar wasannin jami’o’i ta kasa wadda akafi sani da NUGA.
An tabbatarda nadin nashi a lokacin babban taron hukumar NUGA da akayi a tsakanin 17 da 18 na watan Afirilu a jami’ar Jos.
Farfesa AA wanda shehun malamine a sashin wasannin da motsa jiki na jami’ar Bayero ta Kano, kwararrene a farnin kuma mai dinbin basira, hikima da aiki tukuru.
Nadin wanda ke da waadin shekaru biyu ya fara aiki tun daya ga wannan watan na Mayu.
Allah ya taya riko, ameen.