Bayan dakatar da kocin Kano Pillars watau Evans Ogenyi da mataimakinsa Ahmad Garda Yaro Yaro daga aikinsu, hukumar gudanarwar kungiyar ta sanarda nada tsohon kociyan kungiyar cs=0&sca_esv=4acce884baa46368&sxsrf=AE3TifO5n1ObDsJdQPcZN0rF_8yMC-I0Rg%3A1761127271445&q=Mohammed+Babaganaru&sa=X&ved=2ahUKEwj1i4-rxreQAxXqRKQEHRv1M9kQxccNegQIAhAB&mstk=AUtExfAuvwheQOBr0g2Zz8ZwzKC1dgvqWa02Q0pkcHSG-3e3PX3OCTbOMWh9hBwNXMQPEffd0RTJXedjB2sxJkA76oLzrCGgy9v2E_3nXLxoCKeFRMzwjyprxgn8-A2OCqjiIWVNigbLDPv_aBwQfQ70w7kDh8WbChK4HzX9TOl0NgSoFcw&csui=3″>Mohammed Babaganaru a matsayin sabon mai horaswar kungiyar na wucin gadi.
Nadin Babaganaru ya tabbata ne jiya da daddare bayan ganawa dashi da zummar fitar da kungiyar daga halin ni yasu da take ciki a wannan kakar wasan ta 2025/26.
Bayan amincewa da dukkan sharudan juna Babaganaru ya yadda da karbar aikin kungiyar da kuma alkawarin fidda Kano Pillars daga cikin halin da take ciki.
Shidai Babaganaru ba sabon zuwa Kano Pillars bane domin a baya ya rike kungiyar har kuma yayi nasarar cin kofi har sau biyu watau 2011/12 da kuma 2012/13.
Amma saidai tun da yabar Kano Pillars shekaru masu yawa baaji amo da tasirinsa a wata kungiya ba balantana a san ingancin aikinsa.
Ko shi Evans da kungiyar ta dakatar ban tsammani tunda ya bar Kano Pillars bayan sun sami damar komowa Pirimiya ya sami wani ko wata kungiya ba, a zaune yake kamar yadda shi Babaganari yake kafin tabbatar masa wannan aikin.
Na yarda Ganaru yayi nasara a lokacin da yake Kano Pillars amma bayan barinsa Kano Pillars ai kungiyar El-Kanemi Warriors ta Maiduguri ya koma amma fa baici wani kofi ba ko kuma yin abin azo a gani ba.
Ko da barinsa El-Kanemi kungiyar kwallo kafa ta Gombe United ya koma a inda ya ajiye aki da nunin rashin kudi na gudanar da kungiyar da kuma gazawar kungiyar na zuwa wasannin waje.
Dag kungiyar Gombe United Babaganaru komawa kungiyar Akwa United wanda anan ma ajiye aiki yayi a shekarar da ya kama aiki saboda ganin kungiyar ta taho faduwa.
Daga nan Muhammad Babaganaru kungiyar Lobi Stars ya koma a shekarar 2025 amma a can dinma aikin dan takaitaccen lokaci yayi ya ajiye musu aikinsu.
Daga wadannan bayanai zamu iya ganewa cewa Muhammad Babaganaru bashi bane zabin da yakamata, saboda dadewarsa babu kungiya amma tunda anyi mai yiwuwa sai kuma ayi masa abinda yakamata don yayi nasara.
Kwamitin gudanarwa ya sani shi wannan sabon mai horaswar bashi bane zai buga wasa, sai dai yan wasan da kungiyar tayiwa rijista wanda bayanai na nuna rashin ingancin da dama daga cikinsu.
Ida har anaso shi Babaganaru yayi nasara wajen ceto kungiyar daga faduwa (Allah ya kiyaye), sai an bashi duk wani taimako da damar da yake bukata nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
Abu na fari shine a bashi damar duba kungiyar sosai da kuma yan wasan dake cikinta da zummar yin tankade da rairayar wadanda zasu iya da kuma akasin hakan.
A kuma bashi damar nemo karin yan wasan da kungiyar take bukata don karfafa kungiyar ba tare da bata lokaci ba.
A sani cewa a halin da ake ciki yanzu babu ishashshen lokaci don haka ko makwabtanmu watau Niger, Togo, Benin da Ghana a iya dubawa don samo zakakuraen yan wasan da zasu cike gurbin wadanda zaayi waje dasu.
Na kuma sami labarin rashin biyan yan wasa kundin (Match Bonus) har guda biyu, to yakamata a gaggauta biyansu wadannan kudade domin suma suna karawa yan wasa karsashi.
A karshe a nunawa gwamnatin jiha hikima da amfanun kai yan wasa da shugabanninsu zuwa wasanninsu na waje a jirgin sama kamar yadda kungiyar takeyi.
A ganina idan kungiyar Barau zata iya, banga dalilin da gwamnati sukutum ba zata iya ba. Allah ya taimaka.