Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Kamata yayi Pillars su sa kulunboto a bayansu

      December 3, 2025

      KMC outshines MAKIA to win 2025 NDLEA Chairman’s Cup

      November 23, 2025

      NFF: Collection of underperforming football administrators

      November 17, 2025

      Northwest Varsity Kano shines at NUGA…wins three medals

      November 15, 2025

      … As Female Basketball Team storms Semi-Finals

      November 15, 2025
    • Column

      AFCON 2025: Whither Nigerian referees?

      December 1, 2025

      If Barau can do it, Pillars too can do it

      November 24, 2025

      Disappointing Outing: Sacking Kano Pillars’ Management, not solution

      November 17, 2025

      My Reflections on Adamu’s Kano Pillars’ poor performance views

      November 10, 2025

      Fitness Test: Over 1,500 Referees, Assessors to converge in Kano ‘morrow

      November 7, 2025
    • News & Media

      2025 CIPPON Annual General Meeting (AGM) to Hold in Kano

      November 22, 2025

      Congregation Election: ADUSTECH’s NASU, SSANU candidates triumph

      November 18, 2025

      Retirement: Dantiye congratulates Yakasai

      November 14, 2025

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Ibrahim Shekarau

      November 5, 2025

      70th Birthday: Dr. Muhammad Felicitates with Sen. Shekarau

      November 5, 2025
    • Analysis

      2025 Premier Handball League: Why is Kano absent?

      December 5, 2025

      Wa ke son ganin bayan su Ali Nayara Mai Samba?

      December 1, 2025

      Now that Pillars has at last broken long-standing jinx…

      November 26, 2025

      To escape relegation: Pillars urged to defeat Ikorodu City

      November 23, 2025

      Kano Pillars FC: Ta yaya muka sami kanmu a haka?

      November 21, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    • Advert Rates
    Sports Eye
    Home » Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…
    Sports Analysis

    Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…

    Sani YusifBy Sani YusifOctober 22, 2025
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram

    1Bayan dakatar da kocin Kano Pillars watau Evans Ogenyi da mataimakinsa Ahmad Garda Yaro Yaro daga aikinsu, hukumar gudanarwar kungiyar ta sanarda nada tsohon kociyan kungiyar  Mohammed Babaganaru a matsayin sabon mai horaswar kungiyar na wucin gadi.

    Nadin Babaganaru ya tabbata ne jiya da daddare bayan ganawa dashi da zummar fitar da kungiyar daga halin ni yasu da take ciki a wannan kakar wasan ta 2025/26.

    Bayan amincewa da dukkan sharudan juna Babaganaru ya yadda da karbar aikin kungiyar da kuma alkawarin fidda Kano Pillars daga cikin halin da take ciki.

    Shidai Babaganaru ba sabon zuwa Kano Pillars bane domin a baya ya rike kungiyar har kuma yayi nasarar cin kofi har sau biyu watau 2011/12 da kuma 2012/13.

    Amma saidai tun da yabar Kano Pillars shekaru masu yawa baaji amo da tasirinsa a wata kungiya ba balantana a san ingancin aikinsa.

    Ko shi Evans da kungiyar ta dakatar ban tsammani tunda ya bar Kano Pillars bayan sun sami damar komowa Pirimiya ya sami wani ko wata kungiya ba, a zaune yake kamar yadda shi Babaganari yake kafin tabbatar masa wannan aikin.

    Na yarda Ganaru yayi nasara a lokacin da yake Kano Pillars amma bayan barinsa Kano Pillars ai kungiyar El-Kanemi Warriors ta Maiduguri ya koma amma fa baici wani kofi ba ko kuma yin abin azo a gani ba.

    Ko da barinsa El-Kanemi kungiyar kwallo kafa ta Gombe United ya koma a inda ya ajiye aki da nunin rashin kudi na gudanar da kungiyar da kuma gazawar kungiyar na zuwa wasannin waje.

    Dag kungiyar Gombe United Babaganaru komawa kungiyar Akwa United wanda anan ma ajiye aiki yayi a shekarar da ya kama aiki saboda ganin kungiyar ta taho faduwa.

    Daga nan Muhammad Babaganaru kungiyar Lobi Stars ya koma a shekarar 2025 amma a can dinma aikin dan takaitaccen lokaci yayi ya ajiye musu aikinsu.

    Daga wadannan bayanai zamu iya ganewa cewa Muhammad Babaganaru bashi bane zabin da yakamata, saboda dadewarsa babu kungiya amma tunda anyi mai yiwuwa sai kuma ayi masa abinda yakamata don yayi nasara.

    Kwamitin gudanarwa ya sani shi wannan sabon mai horaswar bashi bane zai buga wasa, sai dai yan wasan da kungiyar tayiwa rijista wanda bayanai na nuna rashin ingancin da dama daga cikinsu.

    Ida har anaso shi Babaganaru yayi nasara wajen ceto kungiyar daga faduwa (Allah ya kiyaye), sai an bashi duk wani taimako da damar da yake bukata nan take ba tare da wani bata lokaci ba.

    Abu na fari shine a bashi damar duba kungiyar sosai da kuma yan wasan dake cikinta da zummar yin tankade da rairayar wadanda zasu iya da kuma akasin hakan.

    A kuma bashi damar nemo karin yan wasan da kungiyar take bukata don karfafa kungiyar ba tare da bata lokaci ba.

    A sani cewa  a halin da ake ciki yanzu babu ishashshen lokaci don haka ko makwabtanmu watau Niger, Togo, Benin da Ghana a iya dubawa don samo zakakuraen yan wasan da zasu cike gurbin wadanda zaayi waje dasu.

    Na kuma sami labarin rashin biyan yan wasa kundin (Match Bonus) har guda biyu, to yakamata a gaggauta biyansu wadannan kudade domin suma suna karawa yan wasa karsashi.

    A karshe a nunawa gwamnatin jiha hikima da amfanun kai yan wasa da shugabanninsu zuwa wasanninsu na waje a jirgin sama kamar yadda kungiyar takeyi.

    A ganina idan kungiyar Barau zata iya, banga dalilin da gwamnati sukutum ba zata iya ba. Allah ya taimaka.

     

    an nada Babaganaru.. tunda
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleTunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…
    Next Article Few minutes in the midst of lawyers
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    2025 Premier Handball League: Why is Kano absent?

    December 5, 2025

    Wa ke son ganin bayan su Ali Nayara Mai Samba?

    December 1, 2025

    Now that Pillars has at last broken long-standing jinx…

    November 26, 2025

    To escape relegation: Pillars urged to defeat Ikorodu City

    November 23, 2025

    Kano Pillars FC: Ta yaya muka sami kanmu a haka?

    November 21, 2025

    Jama’a, a ina muka samo ko koyo wannan kuma?

    November 20, 2025
    Add A Comment

    Comments are closed.

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    2025 Premier Handball League: Why is Kano absent?

    December 5, 2025

    Kamata yayi Pillars su sa kulunboto a bayansu

    December 3, 2025

    Wa ke son ganin bayan su Ali Nayara Mai Samba?

    December 1, 2025

    AFCON 2025: Whither Nigerian referees?

    December 1, 2025

    Now that Pillars has at last broken long-standing jinx…

    November 26, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Advert Rates
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.