Sababbin shugabannin Kungiyar Yan Kasuwar Kurna Babban Layi suna kokarin samarda ingantaccen tsaro a fadin yakin kasuwar, shugaban kungiyar Malam Mustapha Umar Malikawa ya bayyana.
Shugaba Malikawa ya shedawa wannan kafa ta yanar gizo jiya a lokacin da yake bayyana irin tarin ayyukan da shugabancinsa yasa a gaba don cigaban kasuwar day an kasuwar baki daya.
A cewarsa tuni suka tuntubi jami’en tsaro na farin kaya da kuma yan kungiyar tsaro ta Vigilanti don yin yarjejeniyar fara aikin don kare dokiyoyin dukkan yan kasuwar baki daya.
“Mun rubuta takardu yarjejeniyoyin da wadancen masu samar da tsaron don su sa hannun wanda daga nanne zasu fara aikin tsaron”, cewar Umar Malikawa.
“Mun shaida musu a cikin yarjeniyoyin cewa karfe sha daya na dare mukeson su fara aiki su kuma tashi da karfe bakwai na safe kullum”, shugaban ya kara bayani.
Daganan Mustapha Umar Malikawa ya kara bayyanawa cewa talatin ga kowane wata zasu rinka biyan masu aikin kula da kasuwar.
Idan baa mantaba, sabon shugaban wanda har yau bai cika sati biyu da darewa kan mulkin kasuwarba yayi alkawarin ciyarda kasuwar gaba ta hanyar kawo tsarikan cigaban kasuwar daki-daki.