A makon da ya gabatane watau ranar 6 ga watan Satumbar wannanshekarar ta 2024 , mai rikon mikamin shugabancin Gidan Talabijin na Abubakar Rimi(ARTV), Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ta cika kwana dari cif da darewa kan mulkin gidan talabijin din.
Zamanta mai rikon mikamin shugabancin gidan watau (Acting Managing Director) Abubakar Rimi Television (ARTV) ke wuya, Hajiya Hauwa ta farfado da gidan daga dogon suman da yayi saboda rashin kulawa da kuma sassaita ayyukan gidan talabijin din ta hanyar bada shugabanci nagari wanda ya sami rauni daga shugabannin da suka shude.
Babu shakka kwana darin da Hajiya Hauwa tayi tana jagorancin ARTV, kwanaki ne masu tarin albarka saboda darurruwan cigaban da ta kawu gidan talabijin din wanda a lokutan baya ake kira CTV 67.
Kasancewarta shugabar ARTV keda wuya, Hajiya Hauwa ta fara saitawa maaikatan gidan alkibla don su rinka zuwa aiki da kuma tashi akan lokaci.
Nan take ta dakatarda zuwa aiki a makare da kuma fashin zuwa aiki wanda a lokutan baya yasha kan gidan.
Tunda masu iya magana suna cewa, daga na gaba ake ganin zurfin ruwa, Hajia Hauwa ta fara nuna kyakkyawan misali wanda yasa ita ke fara zuwa aiki kullum don nunawa sauran maaikatta abinda ya kamacesu.
Jagoriyar ta gyara dangantakar shugabancin gidan da dukkannin ma’aikata wanda shine musabbabin samun dinbin nasarorin da ta samu a wadannan kwanaki dari masu tarin albarka. Saboda kowane maaikaci a halin yanzu na aiki tukuru da kuma kula da kuma bin nagabansa.
Sanin mahimmancin ma’aikatane yasa Hajiya Hauwa daukar hakkokinsu da muhimmancin gaske wanda yasa ta sasu a gaba da kuma gabatar dasu a duk lokacin da aka kawo mata gabanta.
Haka kuma shugabancinta ya samawa gidan sababbin kayayyakin aiki na zamani a kusan kowane bangare da suke bukatarsu don inganta ayyukan ma’aikatan.
Hakan yasa daukacin maaikatan gidan talabijin din ARTV tashi tsaye da kuma daukar aikinsu da mahimmanci ba dare ba rana wanda ya kyautata sauti da kuma hotunan da talabijindin take yadawa.
Wani abu daya da Hajiya Hauwa Isa Ibrahim shine, macece mai haba-haba da kowa da kowa amma bai hanata tsawatawa ba domin batason wasa da aiki.
Saboda tabbatar da cewa ayyuka na tafiya daidai, Hajiya Hauwa ta aiwatar da gyare-gyare a dakunan dakunan yada labarai na gidan (Studio) da kuma samarda na’urorin daukar hotona da kuma komputoci na kan tebur (Desktop) da na kuma kan cinya (Laptop) duk don samun saukin aikin maaikatan gidan.
Hajiyar ta kuma samarda manya-manyan abubuwan saukewa da kuma ajeye labarai, hotuna da kuma fina-finai don amfani dasu nan take ko kuma nan gaba.
Ta samarda sabuwar na’urar wuta (transformer) da kuma gyara injin bada wuta na wucin gadi don samun wutar lantarki akowane lokaci.
Bakamar da ba, Hajiya Hauwa tayi nasarar mayar da shirye-shiryen gidan talabijin din ARTV awa ishirin da hudu ba dare ba rana, al’amarin da yasa gidan samun karin masu kallo a fadin duniya bakai daya. Abinda yasa Hajiya Hauwa zama shugabar gidan ta farko da ta ciri tuta da samun yabo ta ko’ina a fadin yakin jiharnan da kuma duniya baki daya.
Hajiyar wadda mafi yawan mutane ke mata kirarin “Mace mai kamar maza” saboda kokarinta da kuma aikitukurunta ta kuma sami nasarar dora shirye-shiryen gidan ARTV din kan Tauraruwar NIGCOM SAT abinda yasa ganin shirye-shiryen gidan ARTV din a dukkannin fadin duniya.
Hajiya Hauwa ta kuma zamanantar da shirye-shiryen gidan talabijin na ARTV ta kuma yada ayyukansa kan kafofin sadarwa na Twitter, Instagram, Facebook, da kuma TikTok, al’amarin daya karawa gidan masu kallo, saurare da kuma karanttawa a fadin duniya baki daya.
A halin yanzu Hajiya Hauwa ta kuma maida ARTV kafa ta farko wajen nunawa da kuma tallata dariruwan ayyakan alheri da mai girma Gwamnan jihar Kano, Injiya Abba Kabir yaketa aikatawa a fadin jihar Kano.
Wannanne yasa a lokacin da mai girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido kwanan baya, gwamannya yaba mata sosai saboda ganin ayyukan da ta aiwatar da kudaden da ya sahale mata don gyara gida ARTV din.
A dukkannin bangarorin daya ziyarta, gwamna sai murmushi yake tayi saboda gamsuwa da abubuwan da yaganewa idanunsa.
Don haka jamaa da dama ke adduar cigaba, nasara da kuma daukaka ga Hajiya Hauwa a dukkannin ayyukanta da kuma inda ta sami kanta yanzu da kuma nan gaba.
Haka kuma, soyayya da kuma kaunar gwamna yasa ta daukar nauyin gabatar da bikin wasan gasar kwallon kafa ta kananan hukumomi 44 na jihar Kano saboda murnar cikarsa shekara daya a bisa mukin Kano.
A karshe dole a godewa mai girma gwamna wajen zakulo ita Hajiya Hauwa Isa Ibrahim da kuma dora ta kan wannan mukamin. Ga kuma bata hadinkai a inda yake amincewa da dukkannin abubuwa da ta kawo gabansa.
Fatanmu shine mai girma gwamna ya tabbatar mata da mikaminnata don samun natsuwar da cigaba da inganta ayyukan ARTV da kuma tallata da kuma yada ayyukan mai girma gwamna.

Masha Allah