A lokacin da wasu tsirari marasa kishin jihar Kano ke murna da farin cikin halin da kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ke ciki, wasu da dama na bakin ciki mara misaltuwa da wannan al’amari, kuma na fata da addu’ar ganin karshen wannan yanayin.
Da yawan masu bakin cikin wannan mummunar halin da Kano Pillars ta sami kanta a ciki na hangen wasu abubuwan da suka zama haddasana ga koma bayan kungiyar.
Koda yake ba sabon abu bane ganin kungiyar Kano Pillars a baya dumu-dumu a gasar wasan pirimiya ta kasa, amma na wannan lokacin abin yafi muni saboda wasu dalilai.
Dalilan kuwa sune yadda mahukuntan suka bari mai horarwar kungiyar Usman Abdallah ya subuce a karshen kakar wasa ta bara ba tare dayin saurin maye gurbinsa ba.
READ ON: Tunda Kano Pillars ta nada Babaganaru…
Wasu kuma na ganin rashin samo gogaggun yan wasa don cike gurbin wadanda suka gaza ko kuma suka ko koma wasu kungiyoyin shine babban koma bayan da kungiyar ta samu wanda kuma shine ya jawo halinda ake ciki.
Da yawa kuma na zargin kasancewar kungiyar Kano Pillars karkashin ma’aikatar matasa da wasanni ba ofishin gwamna ba kamar yadda aka saba.
Domin tun lokacin da aka kafa kungiyar Kano Pillars a shekarar 1990, ba’a taba ganinta dumu-dumu a karkashin ofishin kwamishina ba irin wannan lokacin.
Wannan kuwa ya faru ne saboda ba kamar yadda aka saba gani a da ba, yanzu komai daga offishin kwamishina kungiyar take karba.
Hatta motocin da gwamnatin jiya karkashin Abba Kabir Yusuf ta samawa kungiyar Kano Pillars kwamishinane ya rarraba ba gwamna ba.
A wannan lokaci duk wasu bukatun kungiyar ta ofishin kwamishina suke fitowa ba daga ofishin gwamna ba, al’amarin da yake damu da daurewa magoya baya da yawa.
Don nemo hakikanin abubuwan da suka da baibaye kungiyar da kuma samo maganinsu, tsohon mataimakain mai horarda kungiyar Kano Pillars, Nasiru Salisu Rasha ya lissafa abubuwa guda hudu wadanda a ganinsa sune matsalolin kungiyar.
A cewarsa, matsalar farko a wajen daukar yan wasa take. A ganinsa yakamata a bar mai horarwa ya neme yan wasan da zasuyi masa aiknsa don samun sakammako maikyau. Kowa ya hakura yabar mai horarwa yayi aikinsa don samun nasara.
A ganinsa aikin shugabannin kungiyar yana wajen fili ne ba cikin fili ba. Jin dadin yan wasa, samarda yanayin walwala ga yan wasa, biyan bonus, kula da lafiyarsu da kuma tabbatarwa kowane dan wasa ya sami hakkinsa sune ayyukan shugabannin kungiyar.
“Ba aikin hukumar gudanarwa ko manaja bane daukar yan wasa. Wannan aikine na mai horarwa domin shiyasan wanda zai bashi sakammakon da yake so,” cewar Rasha.
Wani abin da yake komar da kungiyar baya a ganin Nasiru Rasha shine bangaranci wanda idan ba’a soke shiba bazaibar kungiyar ta cigaba ba. Kowa dan unguwarsu kawai yakeso badan wata unguwa ba duk kyawu ko rashin kyawunsa.
Abu na uku kuma a cewarsa, shine wajen zama na babban bene (VIP stand). A nan ne ake kulla duk wani abu mara kyau.
Idan cin mutuncin yan kwallo ko mai horarwa ne daga wannan babban benan ake kullo shi. Don ha yake ganin yakamata asan yadda zaayi a rage masu zama a wajen.
Abu nakarshe a cewar Nasiru Salisu Rasha shine daina sa bakin shugabannin kungiyar wajen yan wasan da yakamata su buga wasa. Su bar mai horarwa ya zabi wadanda zasu bashi sakammako mai kyau.
Nasiru Rasha ya kuma bada shawarar kafa kotun tafi da gidanka a cikin filin wasan Sani Abacha don hukunta duk wani wanda aka kama da laifin tayarda tarzoma a lokacin wasanni.
Wadannan a ganinsa sune matsaloli da kuma yadda zaa magance su.
Bincikena ya kuma nunamin wasu hanyoyi da yakamata abi don gujewa daga irin wannan yanayin kamar haka:-
- Gyaran tsarin gudanarwa
Kano Pillars tana bukatar sabon tsari na shugabanci wanda zai mai da hankali kan gaskiya, tsari da kuma ingantaccen shiri. Dole ne a daina siyasantar da harkar ƙungiyar, a bai wa ƙwararru damar gudanar da ita ba tare da tsangwama daga masu hannu da shuni ko gwamnati ba.
- Inganta tsarin koyarwa da horar da ‘yan wasa
Ƙungiyar tana buƙatar kwararrun masu horarwa (coaches) da suka san dabarun zamani na ƙwallon ƙafa.
Hakan zai taimaka wajen dawo da dabaru, dabarun tsaron gida (defense organization), da kuma ingantaccen kai hari (attack transition) da kuma cin kwallo (scoring goals).
- Gina ‘yan wasa daga matasa
Maimakon dogaro da yan wasa daga (agents) yakamata Kano Pillars ta mayar da hankali wajen gina matasa masu basira daga makarantu da ƙananan kungiyoyi. Wannan zai sa ƙungiyar ta samu sabbin jini, ƙwarai, da kuzari.
- Tallafi da kwanciyar hankali ga ‘yan wasa
Ƴan wasa suna buƙatar biyan albashi ko bonus a lokaci, da kuma kulawa da su ta fuskar lafiyar jiki da walwala. Idan aka tabbatar da wannan, za su fi sadaukar da kansu wajen kare martabar ƙungiyar.
- Taimakon magoya baya da haɗin kai
Magoya bayan Kano Pillars suna da rawar takawa sosai. Ya kamata su ci gaba da goyon baya cikin lumana, su guji tashin hankali, domin hakan yana sa hukumar ƙwallon ƙafa ta hukunta ƙungiyar, kuma hakan kan haifar da matsin lamba.
- Shirin dogon lokaci
Dole ne ƙungiyar Kano Pillars ta samar da shiri na shekaru 3 zuwa 5, wanda zai kunshi burin dawowa da martabar Pillars, tabbatar da tsayuwa a Premier League, da kuma samun damar fafatawa a CAF competitions.
