Dubunnan mutanen Maiduguri dake jihar Borno ne suka amfana daga tallafin kayan abinci da sauran kayayaki da Zauren Hadin kan Malamai na Jihar Kano ya kai Maiduguri a matsayin gudunmawa.
Hadakar Malaman sun bayarda tallafinne ta hannun Zauren mai suna (NUSAID Humanitarian Initiative. NUSAID), tare da Hadin gwiwar Kwamitin tallafawa na Jihar Borno.
Tawagar Zauren wanda ke karkashin shugabancin Shehun Malami, Farfesa Muhammad Babangida ta rarraba wanda kiyasin kudinsu ya kama Naira miliyan dari da arba’in da shida (N146,000,000) ga wadanda masifar ambaliyar ta shafa.
Kayan da Zauren ya raba sun hada da kayan abinci da tufafi da abubuwan bukata na yau da kullum kamar su kayan wanki da wanka da kuma tufafi ga wadanda suka jikkata daga ibtila’in ambaliyar ruwa da garin Maiduguri ya fada a kwanan baya.
Zauren ya gudanar da wannan rabon kayayyakinne ga wadanda ambaliyar ta shafa kai tsaye da Asubahin ranakun Juma’a 10 da Oktoba da kuma 11 ga Oktoba, 2024 a makarantar Baba Gana Wakil.
Kayan da a ka raba sun kunshi Shinkafa (12.5 kg) buhu 5, 300 da Maggi, da sabulun wanki da tufafi na maza da mata na manya da kanana sama da (4,000) dubu hudu.
Da isar ayarin garin Maiduguri, ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2024, saida ayarin malaman ya kai ziyaran jajantawa ga gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da kuma Wazirin Borno, wanda ya wakilci Shehun Borno.
A jawabin su na jajantawa, Zauren ya jajanta musu tare da nuna alhinin mutanen jahar Kano baki daya akan wannan ibtila’i tare da yin adduar Allah ya tsare gaba ya kuma mayar musu abinda suka rasa da alheri.
Da yake jin tabakin al’umma da shugabannin garin Maiduguri,wakilinmu ya rawaito mutanen na ta nuna godiyarsu da karamcin da Zauren ya musu da kuma yabawa mutanen Kano akan nuna kauna da soyayya ya da zumunci da suka yi musu.
Mutanen na kuma addua’ar Allah ya sakawa Zuaren da alheri, ameen
Allah ya tsare mu