Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Sports Eye
    SUBSCRIBE
    • Home
    • News

      Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

      October 20, 2025

      Handball: Army massacres Pillars

      October 13, 2025

      Kungiyar Barau: Kuskuren da Ibrahim Canji, mabiyansa suka tafka

      September 30, 2025

      Sauye-sayen kungiyar Barau: Kuskuren Sanata Barau tare dana Canji

      September 25, 2025

      Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

      September 9, 2025
    • Column

      NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

      October 20, 2025

      On Shehu Adamu’s assessment of Kano Pillars’ poor performance

      October 13, 2025

      SWAN: Genuine sports stakeholder than NFF, other federation members

      October 6, 2025

      Changes in Barau FC: Where DSP Barau Jibrin fumbles

      September 29, 2025

      Shehu Dikko one year in office: Is there light in the tunnel?

      September 22, 2025
    • News & Media

      Re-Extortion at Urology Center: Gov Abba must hear this

      October 10, 2025

      Environmental Journalists begin two-day training in Abuja

      September 23, 2025

      Two-day training for environment journalists in Abuja

      September 21, 2025

      To transform smart living in Nigeria: FENAC secure solutions, collaborates with South African firm

      September 17, 2025

      Re-Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

      September 11, 2025
    • Analysis

      Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

      October 20, 2025

      Rashin kokarin Kano Pillars da Barau: Sai fa gwamnati ta yi wani abu

      October 7, 2025

      Barau FC, please wake up.

      September 15, 2025

      Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

      September 9, 2025

      NPFL matches: Gov Abba backs Barau FC, shames pessimists

      August 23, 2025
    • Personality Profiles

      Alhaji Shehu Muhammad Dankadai, Sarkin Shanun Kano

      October 28, 2024

      Engr. Ibrahim Usman Aikawa: New Kano Poly Governing Council’s PAB’s representative

      August 24, 2024

      Aminu Kano 40 years after…

      April 17, 2024

      Ameh Agnes: A woman farmer of repute

      April 15, 2024

      Dr. Usman Ibrahim Aikawa: New Kano Poly, Director Academic Planning

      January 2, 2024
    Sports Eye
    Home » Yadda Little, Maikaba suka tsunduma Kano Pillars cikin rudani, asara, rashin tabbas…
    Sports News

    Yadda Little, Maikaba suka tsunduma Kano Pillars cikin rudani, asara, rashin tabbas…

    Sani YusifBy Sani YusifMay 7, 2024
    Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram

    Hakika kishin jinsi, yanki ko kasa abune mai kyau da tarin tasiri da kyau musamman idan anyi su bisa tsari, hangen nesa da kyakkyawar manufa wadda ba zata cutarda abokan zama, sauran yanki ko makwabta ba.

    Kishin yana zama alfanu ne idan anyishi ne don samowa kai yanci ko kuma fitarda kai daga wani kangi ko takaici da wani sakaci ko rashin ilmi ya jawo.

    Amma shigo da irin wancen kishin cikin abunda baya bukatar hakan abune mai hadarin gaske saboda tarin illolin da zai harfar nan take ko kuma gaba kadan.

    Don haka kasancewar Alhaji Babangida Little shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da kuma kasancewar Abdu Maikaba zama babban mai horarda yan wasan Kano Pillars a wannan zangon na kakar wasa ta bana (kafin dakatar dashi) ya jawowa kungiyar Kano Pillars rudani,  babbar asara da rashin tabbas.

    Wannan ya farune saboda shigo da tsarin daukar yan wasan gida kawai wanda ba wata kungiya ko kasa da ta taba aiwatar dashi kuma takai labari a duk fadin kasarnan, Afirika da kuma duniya baki daya.

    Da farin fari, tsarin da Maikaba ya kawo wanda Little ya amince ko kuma Little ya kawowa Maikaba ya aiwatardashi ya  faranta musu da farko amma daga tsakiya ko kuma karshen karshennan babu wanda tsarin bai bakantawa ko munanawa ba.

    Kowa ya sani cewa shi wasan kwallon kafa bakone, watau kawoshi akayi don haka babu yadda zaa ayi wata kungiya ko wata kasa ta iya samun nasarar da take bukata muddin ta aiwatar da tsarin yan gidanta, ko jiharta, ko yan kasarta kawai.

    Duk da mutane da dama cikinsu harda manyan masu horarda yan wasa  na jiharnan na ganin faidar tsarin na yan gida tsantsa saboda baiwa yan gida aiki da tsarin yayi, amma illar da kuma tsarin yayiwa kungiyar da kuma jiha nada tarin yawa.

    Kaf babu wata kungiya a fadin kasarnan ko duniya da ta aiwatar da irin wanna tsarin na yan gida ko kabilarta ko jiharta tsansta kuma ta kai labari.

    Idan aka dubi manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa na fadin kasar nar babu wata kungiya da tayi tasiri ko kuma sami nasara da tsarin yan gida tsantsa.

    Tarihi ya nuna cewa a shekarar 1953, kungiyar kwallon kafa ta Kano XI ta lashe gasar kasa ta Challenge Cup bayan da ta buge takwararta ta Pan Bank da ke garin Lagos da ci 2-1 a wasan karshe kuma a filin wasa na King George wato filin wasa na biyar da ke garin Lagos wato Onikan Stadium.

    Duk ‘yan wasan da suka bugawa kungiyar Kano XI baki ne, wato ‘yan kabilar Igbo ne wadanda suka hada da mai tsarongida Onyemezie da dan uwansa  Phillip Onyemezie da kuma ‘yan uwa babba da karami wato (Okoh senior and Okoh junior) da Nzeli (Captain) da Maxwell da Agha da Harbour ko kuma Sr, Chukulubi da Paragon da Onyeador da Kunuji da Baba Bruce da sauransu.

    Bugu da kari, a wacan lakacin, Kano XI ce ta mamaye wasan a lardin arewa tun daga 1953 zuwa 1957, ayayin da ta lashe kofin Gwamnan lardin arewa a shekarun 1955 da kuma 1956.

    A wasan kasa da kasa kuma, Kano XI, a shekarar 1957 tayi 2-2 da kungiyar kasar Russia  wace ta zo Nigeria saboda wasan sada zuminci kuma Kano XI ce kurum ba ta yi rashin nasara ba a wasannin da kungiyar kasar Rassis ta yi da kungiyoyin Lagos da na Enugu.

    Haka zalika a shekarar 1964 kungiyar Queens Park Rangers da ke yankin Scotland na kasar Birtaniya tasha kashi a hannun Kano XI a wasan sada zuminci.  

    Kuma a kungiyoyi da aka fara gasar Rukuni-Rukuni a Kano a wancan lokacin, mafi yawansu baki ne wadanda suka hada da Rendezvous da Jalco (Joe Allens) da Young Stars da Zumunta da Post and Telegraphs (P and T) da United Africa Company (UAC) da sauransu.

    A baya anyi yunkuri ko kokarin kafa wata kungiya domin maye wadancan ‘yan wasa da namu na gida kamar su Sidi Fagge wato Sidi coach da Bala Galadima wanda akafi sani da (Aikinka) da Ari da Audu Captain da Ammani Inuwa da Tanko Faya da Haruna Lawali da Dan Kan-Kan da kuma sauran su, wanda hakan ya gagara domin baaci nasara ba.

    A shekarun 1970 zuwa 1980 an sake yin wani yunkurin, a inda aka kafa kungiyar Raccah Rovers a Kano, a wancan lokacin mafiyan ‘yan wasan  Raccah Rovers bakine irin su Iliyusu Yashin da Abdulwahabu Haruna masu tsaran gida da Abubakar Garba da Shafiu Muhammad da Baba Otu Muhammad da Kalala Muhammad da Anas Ahmad da Granson Abbas wadanda duka ‘yan kasar Ghana ne, a inda suka lashe gasar Rukuni-Rukuni ta Nigeria a karon farko zuwa garin Kano a shekarar 1978.

    Haka kuma anyi wani yunkurin ko kokarin maye gurbin wadancan yan kasar Ghana da ‘yan wasan gida a 1984 bayan da Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin sallamar baki ‘yan kasashen waje daga Nigeria.

    A wancan lokacin da aka maye  gurbusu da ‘yan wasan Ghana da namu na gida kamar su Alhaji Rabiu Chanhu wato Farfesa Rabiu Muhammad da Danlimi Usman da Sammani Morning da Nasidi Nido da Nazifi Muhammad da Muhammad Musa da sauransu.

    Shma wancan kokarin bai haifar da da mai ido ba domin kungiyar Raccah Rovers tayi wasa guda 34 a gida da waje amma ba tayi nasara a ko guda daya abinda yasa kungiyar faduwa zuwa Rukuni da biyu.

    A baya nan kuma a shekarun 1970 bayan da aka kammala yakin basasa a Nigeria aka kafa kungiyar Enugu Rangers da ‘yan kabilar Igbo tsan-tsa, a inda kungiyar ta mamaye wasaanni a Nigeria tare da samun nasarori, amma hakan bai dore ba domin tun da kungiyar ta lashe kofin gasar Rukuni-Rukuni a 1984, ba ta sake lashe kofin ba sai bayan shekuru 32 wato a 2016, shima bayan da ta soke tsari na ‘yan wasan gida tsan-tsa.

    Ita kuwa takwararta ta Enyimba International da ke garin Aba ta zama kungiyar kwararru kuma a gasar kwarraru a gida Nigeria, a in da ta debi ‘yanwasan ta a ko inna, wato a gida da waje, wannan ya ba ta damar lashe kofin gasar Rukuni-Rukuni a karo uku a jere wato a 2001 da 2002 da kuma 2003 kuma ya ba ta damar lashe kofin Zakaru kulab-kulab na Afirika a 2002 da 2003 da ‘yanwasa irin su Ahmad Garba Yaro-Yaro, Musa Tsu-tsa da Yusif Muhammad da sauransu.

    Ko a lokacin da aka duba irin kungiyoyin kwallon kafa na su Abiola Babes, Leventic,  Mighty Jets, Ranchers Bees da sauransu ba tsarin yan gida tsantsa sukayi ba.

    A cewar wani masani, “shi wasa wanda ba kune kuka kirkiroshi ba, ba ruwansa da yan gidanci da kuma kabilaanci.”

    Kokarin yin hakan kuwa a cewar masana, zai haifar da babbar asara ga kungiyar ta assasa tsarin wanda zaisa dana sani.

    Irin wannan tunanin na rijistar yan wasan gida tsantsa da  Little da Maikaba suka aiwatar a kungiyar Kano Pillars babban kuskure ne, domin yin hakan ya jefa Kano Pillars cikin ni yasu da kuma asara mai yawa yanzu da nan gaba.

    Dauko dan wasan gidan daga wata karamar kungiya da kuma bashi karamin kudi don sa hannu yayi maka wasa zai zama babbar asara ga kungiyar domin yana gogewa mayan kungiyoyi zasu ninka masa kudin sa hannu wanda babu tantama tafiyarsa zaiyi.

    Wannan zai hafarwa kungiyar gibi da kuma sake renon wani karamin dan wasan wanda shima da ya goge wata kungiyar zata daukeshi. A wannan kadamin an mayarda kungiyar mai reno na ba gayra ba dalili.

    Wani masani na cewa idan kungiyar Kano Pillars da gaske yan gida tsantsa take shaawaryi, abune mai sauki domin dubawa zatayi kungiyoyinmu na gida dana waje ta debo yaranmu da sukayi fice kuma suke wasa a wadannan kungiyoyin.

    “Baza a rasa irinsu a Enyimba, Rangers, Sun Shine, Tornadoes da sauran kungiyoyin ba.” Cewar masana.

    Masanin ya kara da cewa idan mahukuntan kungiyar Kano Pillars da gaske suke, ko a kasashen Afirika da Turai baza a rasa yan wasanmu na gidaba wadanda sunyi fice a wasan kwallon kafa ba. “Su nemo su zasu iya buga musu wasa kuma su ciyo musu kofina,” cewar masanin.

    Bincike ya tabbatar cewa wannan tsarin na Little da Maikaba durkushe kungiyar yayi domin ta koma (breeding ground) watau sansanin kyankyashe yan wasa kawai kuma da wannan tsarin kungiyar bazata taba cin wani kofi ba.

    Nasarar da kungiyar zata samu kawai ta ce ta kyankyashe yan wasa wanda manyan kungiyoyin kwallon kafa zasu rinka daukewa a saukake.

    A baya bayannan  rashin tasirin tsarin ya sake bayyana a lokacin watan Azimin watan Ramadana inda kasancewa dukkannin yan wasannamu yan  gida sauran kungiyoyi sukata wahalar da kungiyar Kano Pillars a duk lokacin da akazo gasar NPFL.

    Don haka ya zama dole a sake lale a sabuwar kakar wasanni ta badi.

    suka tsunduma Pillars yadda Little da Maikaba
    Share. Facebook Twitter Telegram Email WhatsApp Copy Link
    Previous ArticleDa dumi-dumi: Kano Pillars ta dakatar da Maikaba
    Next Article Suspension of UniCross VC sketchy – Dr Peter Inyali
    Sani Yusif
    • Website

    I was a staff of the then Triumph Newspapers, with keen interest in sports journalism which drove me to the unit where I was supported and oiled in the dynamics of modern sports reporting by my mentor/friend, Sani Zaria, the then Group Sports Editor of the Triumph. And when he left in 1995, I tried to sustain the spirit against all odds with a column sportesye. But when The Triumph was closed, I was moved to Kano Polytechnic as a lecturer until my retirement last 3 years, which gives me time to return to what I know best , the recreation of the SPORTS EYE.

    Related Posts

    Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

    October 20, 2025

    Handball: Army massacres Pillars

    October 13, 2025

    Kungiyar Barau: Kuskuren da Ibrahim Canji, mabiyansa suka tafka

    September 30, 2025

    Sauye-sayen kungiyar Barau: Kuskuren Sanata Barau tare dana Canji

    September 25, 2025

    Kano Pillars three games, one point: Stakeholders react

    September 9, 2025

    Gumel, Maizare, others to head newly formed SPS

    August 29, 2025
    Add A Comment

    Comments are closed.

    Stay In Touch
    • Facebook
    • Twitter
    • Pinterest
    • Instagram
    • YouTube
    • Vimeo
    Latest Posts

    Korar Ogenye da Yaro Yaro: Ba su suka kar zomon ba

    October 20, 2025

    Celebrations as SWAN honours Ado Salisu

    October 20, 2025

    NPFL’s unjust and unfair treatment for Kano Pillars

    October 20, 2025

    Handball: Army massacres Pillars

    October 13, 2025

    On Shehu Adamu’s assessment of Kano Pillars’ poor performance

    October 13, 2025
    © 2025 Sports Eye. Redesigned by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About
    • Contact
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.